Home Labarai Bukarti ga Turji: In ka cika jarumi ka fito kayi gaba-da-gaba da sojoji

Bukarti ga Turji: In ka cika jarumi ka fito kayi gaba-da-gaba da sojoji

0
Bukarti ga Turji: In ka cika jarumi ka fito kayi gaba-da-gaba da sojoji

Fitaccen mai sharhi kan lamuran tsaro a Najeriya, Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana jagoran ƴan fashin jeji da su ka addabi Arewa maso yamma, Bello Turji a matsayin matsoraci wanda ba zai iya yin gaba da gaba da sojoji ba.

Bulama na mayar da martani ne bayan kalaman Bello Turji wanda yayi a wani faifan bidiyo a kwanan nan, inda ya ke caccakar Bukarti din.

A sakon da ya wallafa a shafin sa na X, Bukarti ya ce Turji na kokarin kawar da kansa daga matsayin ɗan ta’adda zuwa mai ikirarin kare Fulani, inda ya ce, hakan ba zai yi tasiri ba domin duniya tasan ko waye shi.

“Al’ummar Fulani sun barranta dashi saboda suna ganin sa a matsayin mai lefi dake ɓata musu suna.

“Sannan kalaman na Turji yayi su ne don ɓata irin mu dake tona ayyukan sa na ta’addanci da kuma yin kira ga Gwamnati ta ɗau mataki n soji a kan sa da yaransa.

“Shi ba komai bane, illa matsoraci da yake zaluntar waɗanda basu ji ba basu gani ba kuma ya dinga musu sata kamar ɓera. Idan shi yana jin jarumi ne to ya fito yayi gaba da gaba da sojoji”, inji Bulama.