
Barista Audu Bulama Bukarti, shahararren lauya nan mai fafutikar kare hakkin dan Adam da marasa galihu, ya tsallake matakin samun lasisin aiki a matsayin kwararren lauya a kasar Birtaniya.
Bukarti ya tsallake mataki na biyu wanda kuma shi ne na ƙarshe na samun izinin fara aiki a matsayin ƙwararren lauya a yankunan Wales da New England na Birtaniya, kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito.
Tuni dai Bukarti ya fara karɓar sakonnin taya murna ga wasu shahararrun mutane ta kafafen sadarwa.
Shahararren dan jarida kuma mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya wallafa a shafinsa na facebook, inda ya ce, “Farin cikina ba zai misaltu ba da na samu labari cewa abokin aikinmu kuma dan uwa Audu Bulama Bukarti ya tsallake matakin karshe a Shirin Musayar Kwararrun Lauyoyi.
“Yanzu zai iya neman lasisin aiki a matsayin kwararren lauya a yankin Ingila da kuma Wales. A takaice, zai iya aiki a matsayin lauya a wadannan yankuna.”
Barista Bulama Bukarti, ya yi fice wajen bincike da fashin baƙi a kan ayyukan ta’addancin Boko Haram, kungiyar da ta addabi yankin da ya fito, wato Arewa maso Gabashin Najeriya.
A watan Satumban shekarar 2020 ne dai Cibiyar Tsara Dabaru, Nazari da Bincike kan Harkokin Tsaro na Kasa da Kasa (CSIS) ta nada Audu Bulama Bukarti a matsayin babban lauyanta.
Bukarti gogaggen lauya ne dan asalin Gasua a Jihar Yobe, amma ya yi karatu kuma yake zaune a Jihar Kano, kafin tafiyarsa CSIS.