
Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University, MAAUN da ke Najeriya da Niger, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayyana cewa burinsa shi ne ilimantar da mutane sama da Miliyan 1 kafin ya bar duniya.
Farfesa ya bayyana hakanne a hirar da yayi da kafar yada labarai ta BBC Hausa a yau Lahadi.
Farfesa Gwarzo ya ƙara da cewa yana da kyau jami’o’i na gwamnati da masu zaman Kansu su yi hadin gwiwa wajen kawo ci gaba a fanni ilimi a kasar, Wanda burinsa a Kullum shi ne ya kawo sauyi da ci gaba acikin harkar ilimi a Nijeriya da Arewa baki daya.
Gwarzo ya ce, kawo yanzu ya dau nayin karatun ‘yayan talakawa da suke da kwazon karatu a tsarin tallafin karatu wato scholarship a kasar Niger sun Kai mutum Dubu.
A karshe shugaban jami’ar ta MAAUN, ya bukaci gwamnati ta duba matsalolin da jami’o’in gwamnati ke ciki na yajin aiki domin nan ne kadai Dan talaka yake samun damar yin karatu cikin sauki.