Home Siyasa 2023: Buri na shine na maida Kano cibiyar kasuwancin Afrika — Salihu Tanko-Yakasai

2023: Buri na shine na maida Kano cibiyar kasuwancin Afrika — Salihu Tanko-Yakasai

0
2023: Buri na shine na maida Kano cibiyar kasuwancin Afrika — Salihu Tanko-Yakasai

 

 

Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa yana da burin ya maida jihar ta zama cibiyar kasuwancin nahiyar Afrika gaba ɗaya idan har ya lashe zaɓen gwamna a 2023.

Yakasai, wanda a ka fi sani da Dawisu, ya bayyana haka ne a yayin yaƙin neman zaɓen sa a wasu ƙanan hukumomi na Jihar Kano a yau Asabar.

A cewarsa, kudirorin nasa sun hada da yadda za a mayar da Kano ta zama cibiyar kasuwanci ba kawai a Najeriya ba, har da kasashen Afirka baki daya a cikin shekaru 10 masu har ta wuce jihar Legas.

Yakasai ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ya bar wasu aiyukan cigaba a bangarori bakwai, kamar; bunkasa Tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa, Inganta ilimi, lafiya da muhalli, sai inganta ma’aikatun gwamnati wato yadda za a gyara harkokin mulki gaba daya a jihar da kuma uwa uba inganta tsaro domin samun kwanciyar hankali da lumana.

“Ba wai kawai mun shiga Siyasa ido rufe bane,Muna da manufar bari wani abu da za’a dade ana tunawa dani, kuma hakan ba za ta samu ba sai idan mun mai da hankali wajen samar da ayyukan raya kasa, da kula da bukatun talakawa domin inganta rayuwar su su zamo abun kwatance a Cikin al’ummar Nigeria ” Inji Salihu Tanko Yakasai

“Wadannan hanyoyi ne da muke ganin za mu iya gyara al’amuran Kano da kyau da kuma mayar da jihar zuwa mafi bunkasar tattalin arziki da wadata da za su ciyar da bangarori daban-daban na tattalin arzikin jihar gaba, kamar yadda na ambata wasu muhimman kudirori guda bakwai da Zamu mai da hankali akansu a matsayin manufofinmu.

“Shirinmu cikakke ne kuma burinmu shine, ta yaya za mu sanya Kano ta zama cibiyar inganta kasuwanci ba kawai a Najeriya ba, har ma a Afirka a cikin shekaru 10, ta zarce Legas. Shi ya sa muka kiran shirinmu “Vision”. 2033″.

Tanko Yakasai, wanda yake da kwarin gwiwar lashe zaben ya bayyana cewa, “Abin farin ciki, muna wakiltar rukunin al’umma mai matukar muhimmanci a jihar Kano wato matasa kuma muna da tabbacin cewa su ke da kaso 70% na al’ummar kasar za su zabi wanda zai wakilce su, wanda ya san bukatunsu kuma yake cikinsu.