
Gwamntocin soji na Burkina Faso, Mali da Nijar sun fice daga ECOWAS, inda su ka ce ficewwe ta nan take ce.
A wani rahoto da Vanguard ta fitar, kasashen uku sun ce kungiyar ta ECOWAS ta zamto barazana ga mambobinta.
Shugabannin kasashen uku sun ce ficewar wani mataki ne na kashin kan su a matsayin su na ƙasashe masu ƴanci.
An yi juyin mulki a ƙasashen uku da ke fama da rikice-rikice na yan ta’adda da talauci, tun bayan juyin mulkin Nijar a watan Yulin bara, Burkina Faso a 2022 sai kuma Mali a 2020.