Home Labarai Butulci a Siyasar Kano tsakanin Kwankwaso da Ganduje

Butulci a Siyasar Kano tsakanin Kwankwaso da Ganduje

0
Butulci a Siyasar Kano tsakanin Kwankwaso da Ganduje
Sanata Kwankwaso daga hagu, sai Gwamna Ganduje daga dama

Daga Yasir Ramadan Gwale

Wato wannan sa-toka sa-katse da ake yi tsakanin mutanan Kwankwaso da na Gwamna Ganduje na daya daga abinda yake bani mamaki kuma yake daure min kai, kai gaskiya yana kara sanyawa ma siyasa ta bani tsoro. Babban abinda yake bani tsoro shi ne yadda wasu ‘yan siyasa ke yin Butulci da Bita-da-kulli kuma har hakan ya zama abin alfahari.

Dukkan mutanen da suke tare da Gwamna Ganduje a yanzu, babu wanda a baya bai saka jar hula ya yabi Kwankwaso ba, da yawansu kamar zasu yiwa Kwankwaso bauta, suna ganin Kwankwaso a matsayin Gwarzo, Jagora, Haziki, Jarumi, Jan-Namiji, da damansu sun sha cewar babu sama da shi a Arewa wajen kishi da son kasa da kuma kaunar jama’arsa.

Ba sai mun kama sunaye ba, amma gasu nan, muna tuna lokacin da suke sanye da jajayen huluna, suna kalamai na yabo da jinjina ga Kwankwaso, ashe duk tumasanci ne da neman samun shiga da kuma son abin duniya. Abin akwai ban tsoro da ban mamaki irin yadda wasu wadan da suka zake matukar zakewa a harkar Kwankwaso lokacin da yake gwamna, amma kuma yau su ne suka juya baya a gareshi suke masa zambo da diban albarka.

Kullum ina mamakin yadda mutanan da suke tare da Ganduje a yanzu suke kalamai na suka da aibantawa ga Kwankwaso, kamar basu bane a jiya lokacin da Kwankwaso yake Gwamna suke yin irin dukkan kalaman da suke yi akansa ban a yabo da jinjina, sun kai kamar su yi masa bauta sabida yadda suke nuna masa soyayya da sanya jar hula, a wancan lokacin duk inda ka gansu suna sanye da jar hula alamar sallamawa da kuma mika wuya ga tafiyar Kwankwaso.

Amma yanzu sabida an raba gari tsakanin Gwamna Ganduje da Sanata Kwankwaso, duk wadancan mutane sun manta irin maganganun da suka yi, da jafa’in da suka yi akan wadan da suke hamayya da Kwankwaso. Yau sun juye sune suka fi masu hamayya da Kwankwaso jifan Kwankwaso da miyagun kalmomi, suna aibanta shi, suna yin dukkan kalamai na tur da Allah wadai ga Kwankwaso, kamar ba su ne suke yabonsa a jiya ba lokacin da yake Gwamna! Abin mamaki.

To amma, zance na gaskiya, wanda duk yafi bani tausayi akan wannan al’amari shi ne Gwamnan Kano Ganduje, domin hakan ya tabbatar da cewar shima duk abinda ake masa na nuna soyayya ba gaskiya bane, wadannan mutane da suke kewaye da shi suke zagin Kwankwaso domin samun shiga a wajensa, su ne nan gaba zasu koma suna zaginsa suna masa zambo sabida babu Gwamnati, babbu wani abu da zai gamsar da kai cewar ba zasu yi masa haka ba shima, randa duk Gwamnati ta kare masa.

Su irin wadannan mutane sai ka rasa gane inda suka dosa, basa jin kunyar karya basa jin kunyar jama’a. Misali mu kalli wani mawaki wanda a baya yayi waka yana yabon Malam Shekarau, ina tuna wakar “Saraki Sai Allah” babu irin yabo wanda wannan mawaki bai yiwa Malam Shekarau ba, amma da Gwamnatin Shekarau ta kare, aka shiga ta Kwankwaso me ya faru? Waka yayi yana cewa “Duna Wakilin Arna” yana jingina hakan ga Malam Shekarau, yayi dukkan kalamai na batanci ga Malam Shekarau (mutumin da ya dinag yabo a baya) a lokacin ‘yan Kwankwasiyya suna tafi suna shewa.

Bayan wani lokaci ba mai tsawo ba, wannan mawaki yanzu ya koma babu wadan da yake yiwa zambo da cin mutunci da cin zarafi kamar Kwankwaso, mutumin da ya dinga yabo a jiya yana kushe Malaman Shekarau da ya yaba a shekaran jiya, wannan mawaki yana waka yana zambo ga Kwankwaso da mutanensa, ‘yan Gandujiyya suna jin dadi suna tafa masa.

To misalin wannan mawaki shi ne misalin da yawa daga cikin ‘yan siyasar da suke tare da wannan Gwamnati ta Ganduje, suna yabo ga Gwamna suna nuna babu wani sai shi, yana jin dadi yana yaba musu yana basu mukamai da kudade suna abinda suka ga dama. To amma, kamar yadda wancan mawaki ya yabi Malam Shekarau kuma ya koma yana masa zambo, sannan ya yabi Kwankwaso sannan shima ya koma yana masa zambo a yanzu, to haka nan zai koma yana yiwa wannan Gwamnan zambo idan Gwamnatinsa ta kare. Musamman ma Gwamna Ganduje da yake da abin fada masu yawa.

To gaskiya abinda yake bani tsoro da al’amarin siyasar nan shi ne yadda mutane basa jin tsoron Allah, wadan da suke yabonka suke jinjina maka, watarana sune zasu koma cikakkun makiyanka suna zaginka suna maka zambo sabida kawai babu gwamnati a tare da kai. Ace in kana da Gwamnati kaine mai mutumunci, amma daga zarar Gwamnati ta kare kai ne mutumin banza abin yiwa zambo mutane na dariya? Anya kuwa? Ya Allah kada ka sanya mu kasance irin irin wadannan ‘yan Siyasar masu butulcewa ni’ima da manta mutanan da suka taimakesu.