Home Labarai An cafke ɗan jaridar ƙasar Zimbabwe saboda alaƙanta kyautar gumamar kamfai da matar Mugabe

An cafke ɗan jaridar ƙasar Zimbabwe saboda alaƙanta kyautar gumamar kamfai da matar Mugabe

0
An cafke ɗan jaridar ƙasar Zimbabwe saboda alaƙanta kyautar gumamar kamfai da matar Mugabe
Grace Mugabe

Daga Ibrahim Sulaiman

Ɗan jaridar da ya yi rahoto kan cewa Grace Mugabe, ɗaya daga cikin matan Shugaba Robert Mugabe na ƙasar Zimbabwe ta rabawa magoya bayan jam’iyyar da ke mulki ta Zanu-PF kyautar sanhon gumamar dan kamfai.

Da yiwuwar za’a gurfanar da Kenneth Nyangani na jaridar NewsDay gaban ƙuliya da laifin ɓatanci ga matar shugaban.

A rahoton ɗan jarida Nyangani, wani ɗan majalisa na jam’iyyar ta Zanu-PF mai suna Esau Mupfumi ne ya rabawa ‘yan jam’iyya ɗan duros din.

Jaridar ta rawaito cewa ɗan majalisar ya ce “Na haɗu da mai ɗakin shugaban ƙasa, kuma an bani waɗannan kaya don na raba muku.

“Akwai kamfai kamfai da kayan bacci da ta takalma da riguna. Ku zo ku karɓi rabonku da Grace Mugabe ta ce a ba ku.”

Sai dai an ce matsanancin halin tattalin arzikin da ake fama da shi a ƙasar ya sa mutane na sayen gwanjon kayan sawa.