
Cecekuce ne ya biyo bayan halartar wasu bishof-bishof wajen bukin kaddamar da mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyya APC, Kashim Shettima, a Abuja yau Laraba.
Idan ba a manta ba, wasu mabiya addinin kirista da suka hada da kungiyar kiristoci ta Najeriya da kuma Pentecostal Fellowship ta Nijeriya sun yi Allah wadai da tikitin takarar musulmi da musulmi na jam’iyyar APC mai mulki.
Da ya ke mayar da martani kan lamarin yayin da yake zantawa da jaridar The Punch a yau Laraba a Abuja, mataimakin shugaban kungiyar ta CAN da kuma shugabanta na jihar Kaduna, Rabaran Joseph Hayab, ya bayyana malaman kiristancin a matsayin wadanda su ke ikirarin cewa ‘Na Allah’ ne amma sun zama kamar ƴan fim ɗin Nollywood.
Ya ce: “Mutanen da muka gani a bikin kaddamar da Shettima da aka yi fareti a matsayin Bishof mutane ne da ba su da isasshen lokacin koyan yadda ake saka tufafin Bishop. Ku kalli hotonsu da kyau za ku ga wani fim din Nollywood.
“CAN ta yi mamakin dalilin da yasa su ke nuna kwadayinsu a fili. Da farko dai wani labari ya fito wai daga Shugaban CAN na jihar Borno kuma mu ka karyata shi.
“Na biyu kuma, akwai wata karyar cewa BAT (Bola Ahmed Tinubu) da abokin takararsa suna kan hanyarsu ta zuwa ganawa da shugaban CAN wata rana.
“Taron da ba gaskiya ba ne kuma a daren da Shugaban CAN ya kasance a Alabama Amurka yana halartar taron kungiyar Baptist World Alliance wanda