
Babban bankin Nijeriya (CBN) ya shawarci ɗalibai da su yi amfani da tsarin Naira ta yanar gizo, wacce aka fi sani da e-Naira wajen biyan kudin makaranta da sauran kuɗaɗe.
Shawarar ta zo ne a yayin wani taron wayar da kai a kan amfani da e-Naira a Jami’ar Legas a Akoka, Legas.
Darakta, Sashen Fasahar Watsa Labarai na Babban Bankin CBN kuma Kodineta, Kwamitin Ayyuka na Fasaha, Rakiya Muhammed, ta ce taron wani ɓangare ne na ƙoƙarin da babban bankin kasar ke yi na ganin cewa babu wata kungiya ta ƴan Nijeriya da aka hana su damar amfani da kuɗin yanar gizo.
Muhamed, wacce jami’i a ce a Sashen Fasahar Sadarwa na Babban Bankin, Khalipha Nuhu ya wakilta a wajen taron, ta ce: “Mun dade mu na hada hannu da kungiyoyi da cibiyoyi da dalibai da dama a wani bangare na hadafin da muke yi shi ne kawo kowa a cikin tsarin; wato kowane dan Najeriya. Don haka, ba za mu bar kowa a baya ba.
“Dalibai kuma sune makasudin haɗin gwiwarmu da kuma inda mafi kyawun shigar da ɗalibai fiye da a jami’a. Don haka ne ma ya sa muka zo a yau domin tattaunawa da dalibai da al’ummar Jami’ar Legas domin wayar da kan su kan menene eNaira da kuma dora su kan dandalin.