Home Labarai CBN ya baiwa masu POS watanni biyu su yi rajista da CAC

CBN ya baiwa masu POS watanni biyu su yi rajista da CAC

0
CBN ya baiwa masu POS watanni biyu su yi rajista da CAC

Babban bankin Najeriya (CBN) ya umurci duk masu sana’ar POS a kasar nan da su yi rajistar kasuwancinsu da hukumar kula da harkokin kamfanoni (CAC) nan da watanni biyu.

An bayyana hakan ne bayan wata ganawa tsakanin Fintechs da Shugaban CAC na ƙasa, Hussaini Magaji (SAN) a Abuja a jiya Litinin.

Shugaban na CAC ya ce wa’adin watanni biyu na yin rajistar wanda zai kare a ranar 7 ga watan Yuli, ba an yi ba ne don muzgunawa wata kungiya ko daidaikun mutane ba, amma “ya yi daidai da ka’idojin doka da kuma umarnin babban bankin Najeriya.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Hukumar kula da harkokin kamfanoni da kamfanonin Fintech a Najeriya, wadanda aka fi sani da PoS operators, sun amince da wa’adin watanni biyu na yin rajistar wakilansu, ‘yan kasuwa da kuma daidaikun mutane da hukumar ta CAC bisa ga sharuddan doka da kuma umarnin babban bankin Najeriya.

“An cimma wannan matsaya ne a yau yayin wata ganawa tsakanin Fintechs da babban magatakardar hukumar ta CAC, Hussaini Ishaq Magaji, a Abuja.