Home Labarai CBN ya yi biyayya ga Kotun Koli, ya bada umarnin ci gaba da tsoffin kuɗi zuwa 31 ga Disamba

CBN ya yi biyayya ga Kotun Koli, ya bada umarnin ci gaba da tsoffin kuɗi zuwa 31 ga Disamba

0
CBN ya yi biyayya ga Kotun Koli, ya bada umarnin ci gaba da tsoffin kuɗi zuwa 31 ga Disamba

Kwanaki 10 bayan da Kotun Ƙoli ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi na naira har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023, babban bankin Najeriya, CBN, ya bi umarnin, inda ya ce za a ci gaba da kashe tsoffin takardun Naira na N200, N500 da dubu N1,000 za su ci gaba har zuwa wa’adin.

A cikin wata sanarwa a jiya Litinin da daddare, kakakin CBN, Isa AbdulMumin, babban bankin ya umarci bankunan kasar da su bi wannan umarni.

“A bisa biyayya ga umarnin kotu da bin kuma doka da oda da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi, gami da tsarin ayyukan Babban Bankin Nijeriya (CBN) a matsayin mai kula da harkokin bankuna, an umurci bankuna a fadin ƙasar nan da su bi hukuncin da kotun koli ta yanke na ranar 3 ga Maris, 2023.

“Saboda haka, CBN ya gana da kwamitin ma’aikatan banki kuma ya ba da umarnin cewa a ci gaba da kashe tsofaffin takardun Naira na N200, N500 da N1000 tare da waɗanda aka sake wa fasali har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.

“Saboda haka, an umurci duk wanda abin ya shafa da su bi tsari yadda ya kamata,” in ji sanarwar.