Home Labarai CBN ya dakatar da karɓar caji a kan ajiyar kuɗi sama da dubu 500

CBN ya dakatar da karɓar caji a kan ajiyar kuɗi sama da dubu 500

0
CBN ya dakatar da karɓar caji a kan ajiyar kuɗi sama da dubu 500

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da karbar kuɗin caji daga masu ajiye kuɗi a asusunsu na banki, waɗanda suka kai sama da naira 500,000, daga yanzu har zuwa ranar 30 ga Afrilu, 2024.

Babban Bankin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun mukaddashin daraktan sanya ido kan harkokin bankuna, Adetona Adedeji.

A shekara ta 2019, babban bankin ya bayyana cewa zai fara cire wa masu mu’ammala da banki kuɗi a lokacin da za su cire ko ajiye kuɗi a banki a wani bangare na kokarinsa na rage amfani da tsabar kuɗi.

A baya, babban bankin ya umarci bankuna su riƙa karbar kashi biyar bisa dari na kudaden da za a cire da kuma kashi uku cikin dari na kuɗaɗen da za a ajiye sama da naira miliyan uku.

Sai dai, a cikin sabon umarnin da ya bayar, babban bankin ya ce, ya kamata bankunan su karbi dukkan kudaden da jama’a ke ajiyewa a banki ba tare da wani caji ba.

BBC Hausa