Home Labarai CECEKUCE GAME DA HARAJIN KULA DA INTANET — Sanarwa ga Manema Labarai

CECEKUCE GAME DA HARAJIN KULA DA INTANET — Sanarwa ga Manema Labarai

0
CECEKUCE GAME DA HARAJIN KULA DA INTANET — Sanarwa ga Manema Labarai

CECEKUCE GAME DA HARAJIN KULA DA INTANET

Sanarwa ga Manema Labarai

Daga SANATA SHEHU BABA UMAR: Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai da Sha’anin Tsaron kasa da Tattara Bayanai.

1.A matsayina na Shugaban Kwamitun tsaronda tattara bayanai na Majalisar Dattijai na Najeriya an ja hankalina sakamakon cecekuce da ya biyo bayan bayanan Babban bankin Najeriya na kokarin aiwatar da Harajin game da kiyaye tsarin harkar tafiyar da Intanet a Najeriya(kamar yadda Dokar ta tanada Da Zata hana aikata manyan laifuffuka ta Intanet wadda akayiwa kwaskwarima ta shekarar 2024).

2..Wannan Sanarwa ta manema Labarai da ba zaa fitar da ita ba amma sakamakon kudiri na yiwa Dokar gyara tun Shekara ta 2015 wadda wannan Kwamiti ya kirkiro Wanda a halin yanzu ni ne nake shugabantar sa tare da hadin gwiwar Kwamitun fasar sadarwa wato ICT da na Kula da Tsaron Sashin Intanet ,saboda hakane na ga ya kamata a fitar da bayanai yadda suke domin gudin molanka da yiwa al’amura kudin goro ba tare da nutsuwa ba.

3. Tare da girmamawa ya kamata al’umma su Sani cewa kwaskwarima da akayi wa ita wannan doka ta Cyber security an yi ne domin manufar Yan kasa gabaki daya da kuma kokari da ke na ceto kasar nan daga matsalar tsaro wacce ta ki ci taki cinyewa,wanna anyi haka ne domin a magance wani wawakeken gibi da Dokar ta bari da Kuma manufar ingantawa da karfafa kasar mu ta Najeriya domin aiwatar da shirin nan na tsare kafafen sadarwa na Intanet domin inganta tsaro.
4. Sannan daga cikin ayyukan Kwamitun ya bijiro dasu Dan yiwa Dokar kwaskwarima shine rashin wadatattun kudin da barazanar tsaro da Sashin Intanet yake yiwa tsaron kasa da Kuma wasu Muhamman ababan more rayuwa da suka shafi tattalin arzikin kasa.
5)Dokar Gama laifuffuka Ta Intanet(wato ta harmatawa da dakilewa) ta Shekara ta 2015.

Ita wannan doka wacce aka yiwa gyara tana da tanadaddun dokoki na Saka Harajin Hana laifuffuka ta Intanet tun Sanda aka amince da Dokar a Shekara ta 2015.amma babban abunda ya Hana Dokar aiki shine rashin fahimtar tanade tanaden dokar na sanshi na 44 Wanda a da ya sa akayi tayi mata fahimta iri daban daban har zuwa wanna lokaci da akayi mata kwaskwarima da kyakkyawar manufa a Shekarar 2024.

Bayan haka ita babbar Dokar davta Shafiu aikata laifuffuka ta kafar Intanet ta shekarar 2015 ta Kuma tanadar da tsaro na shariah domin dubawa da tabbatar da Dokar tsare kafafen sadarwa na Intanet da sauran dabaru da Kuma Kare Muhamman bayanai da suka shafi kasa,da ya hada da bin tsarin dokoki na Tsaron kafafen sadarwa na Intanet ko yi mata kutse ba bisa kaida ba,da kawo rahoto na yiwa kafar intanet kutse da binciken yin hakan da kuma masu aikata laifuffuka ta intanet tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

6) Haka Kuma wahalarwa da yiwa Al’umma bayani game da tanade tanaden dokar laifuffuka ta Intanet ta shekarar 2015 ya kawo tsaiko na kokarin Karewa da Tsaron kafar sadarwa Intanet duk da yadda gungun masu aikata laifuffuka na sashin yanar gizo suke cin Karan su ba babbaka tare da hadin gwiwar masu aikata taaddanci a Sashin na intanet ta hanyar daukar nauyin su da ake yi.

7. Abu ne Wanda yake ajiye cewa kowa ya San wannan doka ta laifuffuka ta kafar sadarwar Intanet ta shekarar 2024 an yi mata kwaskwarima wacce itace a yanzu ake yiwa lakabi da “Cybercrime (prohibition ,prevention ,etc)Act.No 17 2015” wato Dokar haramta laifuffuka ta intanet,anyiwa dokar kwaskwarima ne saboda a gyara wasu kalmomi da aka goge a Dokar Inda anan ne aka samu shubuha Wanda ake cewa zaa cira Kashi 0.5(0.005) wanda hakan yayi dai dai da cire kasa da Kashi Daya na hadahadar kudi da Dan Najeriya Yake yi ta Wayar hannun ko naurar Computa kamar yadda aka bayyana a sashi na biyu kamar yadda aka bayyana a kasa.

I. Haka Kuma abune sananne cewa akwai wasu gajerun kalmomi da jumlolinda baa fassara ba a cikin Dokar da suka hada da “0.005” Wanda itace asalin shubbuhar da ta kunno Kai Amma yanzu an fayyace bayanai akanta a sabuwar Dokar.

4. Ba tare da Bata lokaci ko dauke hankalin Al’umma ba tanade tanaden dokar cire Harajin Kare kafafen sada Intanet Yana cikin Babban kudin Dokar tun ta shekarar 2015 Amma Gwamnati Bata aiwatar da tanade tanaden dokar ba saboda rashin gamsassun bayanai ,da Kuma yadda zaa aiwatar da ita.

5.Kamar yadda aka Sani ana sauraran raayin jamaa Kafin a amince kudiri ya zama doka saboda haka wannan doka ta magance laifuffufka a Intanet wacce akayi wa kwaskwarima ta shekarar 2024 ita baa bar ta a baya ba sai da aka samu halartar mutane daban daban daga fannoni na rayuwa domin su shaida hakan.

6.Domin tabbatar da anyi gaskiya a kokarin da akayi waken aiwatar da Dokar gaba daya majalisun kasa wato ta Dattijai da ta wakilai sun Zauna sun amince da kudirin na Dokar Hana laifuffuka ta Intanet ya zama doka .

7.Tare da girmamawa GA Yan Najeriya Ina so in shaida musu cewa karancin kudaden da Kuma rashin Bawa tsarin tabbatar da tsaro a harkar Intanet a Najeriya shine Babban dalilin da yasa aiwatar da Dokar ta samu tazgaro Wanda hakan yasa ake ta samun karuwar laifuffuka na cikin gida a kafar sadarwa ta Intanet ,da hare hare da ake samu na Intanet GA Yan Najeriya da Kuma barazanar taaddanci.

8.saboda haka aiwatar da Harajin Kare kafar sadarwa ta Intanet abun ne da ake Bukatar sa cikin gaggawa kamar yadda ake bukar tar wadataccen abinci kamar yadda Shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kwannanan.

9.Saboda haka Yana da matukar muhimmanci a samar da kudade domin daukar nauyin Kare Muhimman guraren Adana bayanai na kasar mu ta Najeriya,da magance taaddanci da Kuma tsattsauran raayin ,karfafa tsaron kasa,da Kuma Tattalin Arziki na kafar sadarwa ta Intanet Amma haka zai yuwu ne ta hanyar tabbatar da an samar da kudade na Karen kafar Intanet ta Najeriya daga matsalar tsaro ga duk masu ruwa da tsaki a harkar kamar yadda yake a sashi na biyu na Dokar.

10.Bayan haka Ina da yakini cewa yin amfani da alkinta Harajin Kare kafar Intanet daga barazanar tsaro a Najeriya zai sa a aiwatar da da sabuntawa da habak manya manyan bangarori na Tattalin arzikin Najeriya da kuma kare kafar Intanet ta Najeriya .

11.ina so In shaida muku cewa kare Sashin Intanet na Najeriya da Kuma tabbatuwar Najeriya wajen hada hada a kafar Intanet shine zai Saka a samar da hanyoyi da kudade da Kuma fadada tsarin lafiya ga kafar Intanet ta Najeriya kamar yadda Gwamnatin Tarayyar Najeriya take Shirin yi a yanzu tare da goyon bayan abokan aiki na na Majalisar kasa.

12.Bayan haka Ina so in sanar muku da cewa bayanai sun tabbatar da cewa barazanar da ake yiwa kafar Intanet ta Najeriya ya ma wuce laifuufukan da ake aikatawa a kafar ta Intanet kamar yadda aka bayyana hakan a tsarin dabarun Kare Sashin Intanet na Najeriya.

13.Ina Kara shaidawa Al’umma cewa idan har muna so kasar munta tsiya tsarin mu na yanzu da muke bi na Kare kafar Intanet daga barazanar tsaro Yana da rauni indai ba mu tashi tsaye mum rungumi Kare Sashin na kafar Intanet ba.

14.Saboda haka ya zama dole Najeriya ta dauki nauyin bawa kafar Intanet kariya da Kuma yaki da taaddanci ba tare da ta Nemi taimakon kasashen waje ba.Domin ya zama wajibi Najeriya ta jajirce wajen mallakar tsare sashinta na Intanet ba tare da taimakon wata kasa ba domin tabbatar da ikon mu a matsayin kasa.

15. A bangaren mu na Yan Majalisa masu yin dokoki ya zama wajibi muyi aiki tare da sauran bangarori na Gwamnatin domin tabbatar da gaskiya da shigo da kowa da kowa domin samun nasarar tsare kafar Intanet ta Najeriya.

16.Saboda haka Ina yarbawa ofishin Mai Bawa Shugaban kasar shawara a harkokin tsaro tare da Babban Bankin Najeriya domin kirkiro tsarin harajin baiwa kafar Intanet ta Najeriya kariya daga barazanar tsaro.Ba wai rigimar ba ce ko damuwa gane da labarin samar da Harajin Kare kafar Intanet ta Najeriya ya kawo cecekuce a wasu bangarori na Najeriya domin amfana da zaa yi da Harajin ya dama ya shanye rashin amfanin.

17.Ina so in sanar muku da cewa duk da ambawa bankunan Najeriya umarnin awaitar da tanade tanaden dokar cire Harajin Kare kafar Intanet ta Najeriya ta Shekara 2024 ina shaida muku cewa ita Dokar ta Saka tausayi kamar yadda aka tanada ,saboda haka wadanda suka aiwatar da Dokar sum fitar da wasu tsare tsare na cire wasu daga Harajin kare kafar intanet daga barazanar tsaro kamar haka.

I.masu raba bashi da kuma biya.

II.Biyan albashi.

III. Tura kudi tsakanin asusun banki na Mutum Daya a banki guda Daya ko Kuma a bankunan daban daban na Mutum Daya .

IV.Tura kudi a banki iri Daya tsakanin masu amfani da bankin.

V.Sai Kuma yadda sauran hukumomin hada hadar kudin zasu bayar da umarnin hada hadar kudin ga bankunan da suke Mu’amala da su.

VI. Hada hadar cikin banki.

VII.Tura kudin da bankuna zasu ga Babban bankin Najeriya.

VIII.Tura kudi tsakanin rassan bankuna a cikin banki daya.

IX.Duba cakin kudin da tsara shi .

XI.Tsarin sake fasalin bashing bankuna.

XII.Sai Kuma masu Ajjiyar kudade da hada hadar kudin da ta dade kamar zuba jari,da kudaden asusun hukumomin Dake bankuna,da na yarjejeniya sai Kuma takaddun kasuwanci..

XIII.Sai Kuma hada hadar kudaden Gwamnati na walwalar jamaa kamar biyan kudaden Yan fansho.

XV. Hada hadar kudade ta manyan makarantun Gwamnati da ya kunshi biyan kudade na jami’o’i
da sauran manyan makarantun gwamnati.

XVI. Hada hadar kudade da ta hada da asusun ajiya na cikin bankuna, kamar wani asusu da ake da tuhuma akansa, asusun ko ta kwana da sauran asusun ajiya masu kamanceceniya da irin wadannan.

18. A wannan halin da ake ciki na rashin tabbas, dole ne a tsame wasu daga cikin wannan tsari domin a samu aiwatuwar wannan tsarin na tsaron kudade ta intanet ya zama yayi nasara.

19. Daga karshe, yana daga cikin aikin wannan kwamiti namu, ba kawai duba dokoki ba har da kawo sabbin tsare tsarem da za su ciyar da wannan kasa tamu Najeriya gaba.

20. Amadadin wannan kwamitin na tsaro da tattara bayanai, Ina mai neman goyon bayan ‘yan Najeriya domin ganin tabbatuwar wannan tsari domin cigaban kasarmu, kuma alumma su amfana da wannan shiri cikin kankanin lokaci.

21. Haka kuma, a madadin majalisar dattawa gaba daya da dukkan abokan aikina, ina mai matukar Nona godiya da jinjina ga dukkan wakilan MDAs da kuma dukkan masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen tabbatuwar wannan aiki.

Na gode kwarai.

Sanata Shehu Buba Umar
Shugaban kwamitin tsaro da tattara bayanai