Home Labarai An ceto ‘yan Najeriya 105 a tsakiyar teku a kokarinsu na haurawa zuwa Turai

An ceto ‘yan Najeriya 105 a tsakiyar teku a kokarinsu na haurawa zuwa Turai

0
An ceto ‘yan Najeriya 105 a tsakiyar teku a kokarinsu na haurawa zuwa Turai

Daga Hassan Y.A. Malik

Wata kungiya mai zaman kanta ta kasar Spain mai suna  Proactiva Open Arm wanda ke bada agajin gaggawa ga bakin haure ta bayyana ceto ‘yan Nijeriya 105 da wasu ‘yan kasasshen Afrika sama da 300 makale a tsakiyar  tekun Meditarranean kusa da Libya

Kungiyar ta gano bakin hauren makare a cikin jirgin da ke rito a yayin da su ke kokarin tsallake teku zuwa kasar  turai kamar yadda ABC News ta bayyana.

Daya daga cikin bakin hauren ya bayyanawa wani dan jarida cewa wasu ‘yan sumoga da ke sufuri a wani jirgi na daban a kan tekun ne suka arce da injin din jirgin nasu, lamarin da ya kai jirginsu ga yin rito a wuri mafi hatsari a tsakiyar tekun

Wannan dai ba shi bane karo na farko da ake ceto bakin haure wadanda ke kokarin tsallakawa daga kasasshen Afrika zuwa kasasshen turai ba inda wasu ma ke rasa rayuwar a yayin wannan bulaguron.

Ko a ranar Lahadi, wata kungiya bada agaji gaggawa mai zaman kanta ta kasar Spain ta kara ceto wasu mutane 476 wadanda duk ‘yan kasar Afrika wanda suka makale a tsakiyar teku a kokarinsu na tsallakawa zuwa kasasshen turai.

Majalisar dinkin duniya dai ta ce mutane akalla mutane 615 ne suka mutu ‘yan kasar Afrika wadanda suka hada da yan Nijeriya a cikin watan Janairu zuwa Afrilu na shekarar 2018 a kokarinsu na tsallake teku zuwa kasasshen ketare.