Home Ƙasashen waje Chadi: Jami’an tsaro sun harbe sama da mutane 60, 300 su ka jikkata a yayin zanga-zanga

Chadi: Jami’an tsaro sun harbe sama da mutane 60, 300 su ka jikkata a yayin zanga-zanga

0
Chadi: Jami’an tsaro sun harbe sama da mutane 60, 300 su ka jikkata a yayin zanga-zanga

 

Sama da mutane 60 ne aka kashe, yayin da wasu 300 suka jikkata bayan da jami’an tsaro suka bude wuta kan fararen hula da ke gudanar da zanga-zangar neman a gaggauta mika mulki ga mulkin dimokradiyya a kasar Chadi.

Jami’an tsaron kasar Chadi sun bude wuta kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati, a cewar wani rahoto na Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da ta’addanci.

An yi wa fararen hular da ba sa dauke da makami kisan kiyashi a yayin da jami’an tsaro suka yi wa masu zanga-zanga mumunar murkushe masu zanga-zanga a babban birnin kasar N’Djamena da wasu garuruwa da dama.