Home Labarai CIKAKKEN LABARI: Abadulmalik Tanko ya musanta garkuwa da kuma kashe Hanifa

CIKAKKEN LABARI: Abadulmalik Tanko ya musanta garkuwa da kuma kashe Hanifa

0
CIKAKKEN LABARI: Abadulmalik Tanko ya musanta garkuwa da kuma kashe Hanifa

 

Abdulmalik Tanko, malamin makaranta, wanda da farko ya amsa cewa ya kashe ɗalibarsa ƴar shekara 5, Hanifa Abubakar, ya yi mi’ara-koma-baya, inda ya ce sam bai yi garkuwa da ita ba, ballantana ma ya kashe ta.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa gwamnatin Kano ce ta maka Tanko da abokan aikata laifin sa biyu, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin, a Babbar Kotun Kano mai lamba 5, inda ta ke tuhumar su da laifuka biyar.

Duk su ukun a na tuhumar su da haɗin baki, garkuwa da mutum, ɓoye wanda a ka yi garkuwa da shi da kuma kisan kai, laifukan da su ka saɓawa sashi na 97, 274, 277 da kuma 221 na dokar ‘Penal Code ta jiha’.

A zaman kotun na yau Litinin, bayan da a ka karanto musu laifukan su, Tanko, a matsayin wanda a ke zargi na 1, da Isyaku, wanda a ke zargi na 2 sun musanta laifukan nasu, ban da tuhuma ta farko.

Ita kuwa Fatima, wacce a ke zargi ta 3, ta musanta dukka tuhumomin da a ka yi mata.

A nashi ɓangaren, lauyan waɗanda a ke ƙara, M.L. Usman, a bisa dogaro ga sashi na 36 (6b), ya nemi gwamnati da taa bashi dukkanin takardun shari’ar domin ya yi nazari sannan a hanzarta shari’ar, inda ya nemi da a ba shi takardun a kasa da mako ɗaya.

Bayan wannan roƙo na sa, sai alkalin kotun, Mai Shari’a Usman Na-Abba ya yarje masa.

Ya kuma ɗage zaman zuwa 2 da kuma 3 ga watan Maris domin sauraren ƙarar.

Sannan Na-Abba ya bada umarnin aikewa da waɗanda a ke zargin gidan yari.