Home Labarai Zaɓen cike-gurbi na Adamawa: Maƙiya demokraɗiyya ne su ka yi min taron dangi — Fintiri

Zaɓen cike-gurbi na Adamawa: Maƙiya demokraɗiyya ne su ka yi min taron dangi — Fintiri

0
Zaɓen cike-gurbi na Adamawa: Maƙiya demokraɗiyya ne su ka yi min taron dangi — Fintiri

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ce ya fafata a zaben gwamnan jihar da makiyan dimokuradiyya da s uka yi masa taron dangi.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a jiya Talata a wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels TV, ya ce masu adawa da shi kawai na son ganin mace ta zama gwamna ba tare da la’akari da ayyukan sa a jihar ba.

Fintiri ya kuma sha alwashin gurfanar da waɗanda su ka aikata laifuka a lokacin zaɓen gwamna a gaban kuliya.

Ya ce: “Ni a gani na ba wai da mace na yi takara a a jihar Adamawa ba. Na yi takara da makiya dimokradiyya da ga wajen jihar Adamawa.

“Rundunar tasu ba ta kai ko’ina ba. Na gode wa Allah. Sun yanke shawarar zama makiyan dimokuradiyya, kuma jihar Adamawa su ke so su ga sun kai ƙasa.

Sun so su saka wata mata daga jam’iyyarsu, sun manta cewa mun yi rawar gani sosai a jihar nan.”

Mista Fintiri, ya ce jama’a sun ki amincewa da a ƙaƙaba musu shugaba, kuma sun kada kuri’a a kan ci gaba.