
A jiya Talata ne kwamitin shiyya-shiyya kan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ya miƙa rahotonsa ga Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar na Ƙasa, NWC.
Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta gano cewa kwamitin bai bayyana matsayar da ya cimma ba.
Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Sen. Iyorchia Ayu ne ya karɓi rahoton kwamitin a Abuja.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Ndudi Elumelu, yayin da yake miƙa rahoton kwamitin ga Ayu, ya ce kowa da ga cikin mambobi 37 na kwamitin ya bayar da tasa gudummawar, inda da ga bisani a ka ɗauki matsaya ta bai-ɗaya.
Ya ce an ɗauki matakin ne domin kare muradun jam’iyyar bisa ka’idojin da kwamitin zartaswa na kasa, NEC ya ba su.
Ayu, yayin da yake karbar rahoton, ya tabbatar wa kwamitin, karkashin jagorancin Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue, cewa za a mika shawarwarin su ga shugabancin jam’iyar PDP na ƙasa domin tattaunawa da kuma yanke hukunci na karshe.
Ya ce za a sanar da ‘ya’yan jam’iyyar a duk fadin kasar nan da kuma daukacin ‘yan Najeriya da ke dakon matakin karshe na kwamitin.