Home Labarai Ciki ya ɗuri ruwa yayin da gwamnatin Kebbi ta fara tantance ma’aikata

Ciki ya ɗuri ruwa yayin da gwamnatin Kebbi ta fara tantance ma’aikata

0
Ciki ya ɗuri ruwa yayin da gwamnatin Kebbi ta fara tantance ma’aikata

 

Gwamnatin Jihar Kebbi ta sanar da fara aikin tantance  bayanan ma’aikatan ta.
Wannan na ƙunshe ne a sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na ofishin Sakataren Gwamnati, Murtala Gotomo ya fitar a Birnin Kebbi a yau Alhamis.
Safiyanu Garba-Bena, Shugaban ma’aikata na jihar Kebbi na wucin-gadi, ya umarci dukkan manyan sakatarorin jihar da su haɗa bayanan ma’aikatan su su kai masa ofishin sa da gaggawa.
Garba-Bena ya ce hakan zai baiwa gwamnati dama ta san adadin ma’aikatan ta sannan ta samu damar cire bara-gurbi.
Ya ƙara da cewa aikin tantancewar zai baiwa gwamnati damar gane cewa biliyoyin Naira da ta ke kashewa wajen albashi na tafiya ne ga ma’aikata na kwarai ko kuma no bogi ne, in ya so sai ta riƙa samun rara na albashi.
Ya kuma gargaɗi manyan sakatarorin da su tabbata sun kawo sahihan bayanan ma’aikatan su.