
Ƙungiyar Haɗin kan O’odua, OPC t anisa ta kan ta daga gamaiyar ƙungiyoyi 57 na Yarabawa da a ka ce suna yaƙin neman a baiwa ɗan yankin Kudu-maso-Yamma masu rajin sauya fasalin Nijeriya a kakar zaɓe ta 2023.
A wata sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na OPC, Yinka Oguntimehin ya fitar, ya nisanta Aare Gani Adams da ga shiga gamaiyar ƙungiyoyin, in da ya ce wannan tafiyar duk cuwa-cuwa ce.
Oguntimehin ya yi kira ga ƙungiyoyin da su dena amfani da sunan OPC a cikin harkokin su domin samun karɓuwa, inda ya jaddada cewa OPC ɗin ba ta cikin waɗannan kungiyoyin 57 ɗin na Yarabawa da su ka yi wata ganawa a ƙarshen mako a Legas domin su haɗa kan yan Kudu-maso-Yamma don goyon bayan takarar Tinubu, Osibanjo ko Fayemi.
Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa an ce OPC ce ta haɗa taron ƙungiyoyi 57 na yankin Kudu-maso-Yamma da manufar haɗa kan yan yankin domin goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar APC da ga yankin a 2023.
An ce wani ɗan jarida, Adewale Adeoye ne ya jagoranci ganawar, inda kuma Sunday Akinnuoye, Femi Agbana da Ganiat Toriola su ka saka hannu a sanarwar bayan taro.
Su dai ƙungiyoyin sun amince cewa su na sane da neman takarar Dakta Kayode Fayemi, Farfesa Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu.
Sun kuma ci alwashin cewa ɗan takara a 2023 zai kasance mai rajin canja fasalin Nijeriya ne kuma wanda zai magance matsalolin ƙasar nan koma a wacce jam’iya zai fito.
Amma kuma Oguntimehin ya ce, babu wani lokaci da OPC, a ƙarƙashin Iba Gani Abiodun Ige Adams da ta haɗa wasu don neman takarar wasu ƴan siyasa, inda ya jaddada cewa manufar OPC ɗin ta wuce iya ka 2023.