
Wata ƴar fim a ma’aikatar fim ta Nollywood, Dorcas Fapson ta ɗora hannu a kai ta na ta gursheƙen kuka, bayan da ta ce direban ta tsere da motar ta ƙirar SUV a ranar bikin murnar zagayowar haihuwarta.
Tuni dai jarumar ta sanya lada ga duk wanda ya kawo bayanai, ko wajen da dirben, mai suna Mohamed ya ke.
“A yammacin zagayowar ranar haihuwa ta. Ina shirin yin biki da ƴan uwa da abokai na, kwatsam sai ma samu labarin cewa direba na ya sace min mota.
“Na sanya lada ga duk wanda ya gano inda Mohamed ya ke ko kuma mota ta.
“Ya yi amfani da lasisi na ƙarya ya yi rijista da wani wakili, wanda tuni a ka kama shi,” jamurar ta wallafa a sahfinta na instagram.
Ita dai Fapson shahararriyar jarumar fim ce kuma mai yin shiri a talabijin, musamman shirin Shuga na MTV, inda ta ke fitowa da suna Sophie.