
Fitaccen malamin addinin kirista na darika Katolika da ke kula da mabiya darikar na yankin Sokoto, Rabaran Mathew Hassan Kukah, ya bayyana cewa kungiyar da tsohon shugaban Nijeriya, Cif Ulusegun Obasanjo ya kafa da nufin samar da canjin shugabanci a kasar nan ba zai taimakawa kasar samun ci gaban siyasa da dimokuradiyyar Nijeriya ba.
A cewarsa, matsalar Nijeriya ba za ta gushe ba kawai don an cire shugaba Buhari daga shugabancin Nijeriya a shekarar 2019, kuma an maye gurbinsa da wani.
Kukah ya ce, samar da wata kungiya da nufin sauya shugabancin Nijeriya saboda wasu kurakurai da shugabancin kasar ke tafkawa ba zai haifar da komai ba sai gaba da rashin aminci a tsakakkanin al’umma.
“Ina ji ai a nan kowa yana da aure ko? In har ku ka ce a duk lokacin da matanku suka ki yi muku biyayyar aure, za ku je ku kara aure, mata nawa za ku aura a rayuwarku? Ina ganin kara aure ba ya magance matsalolin biyayyar aure. Ina muku magana ne a matsayin babban limamin darikar Katolika.”
Kukah ya yi wannan magana ne a yayin da ya ke zantawa da wasu zababbun manema labarai jiya Alhamis a Abuja.
“Matsalar da jam’iyyar APC ke fuskanta a halin yanzu na da nasaba da kasancewarta jam’iyyar hadaka ta ka zo-na zo. Na gani Obasanjo na sanya hannu akan takardar rijista da kungiyar gamayya. Irin wannan kungiyoyin guda nawa muka gani?”
“Ba zai yiwu a ce daga ka yi fushi da ‘yan jam’iyyarka ko kuma an yi zabe jam’iyyarka ba ta yi nasara ba kawai sai ka kafa kungiyar gamayya ko kuma kawai ka canza jam’iyya. Wannan sam ba zai taimakawa dimokuradiyyarmu ba. Ya kamata mu hankalta mu gane cewa a duk lokacin da muka kafa wata kungiya ko jam’iyya, mun sama wadda ta ke nan kafin sabuwar kishiya ne, kuma hakan na nufin samawa kanmu sababbin abokan adawa da haifar da sabuwar gaba.”
“Ba za mu magance matsalar kasar ta hanyar cire wani shugaba mu aza wani ba.”
“Gabanin zaben 2015, ‘yan siyasa sun furta kalaman batanci da basu da iyaka kuma an daura su kafafen yada zumunta na zamani, wanda hakan ko shakka babu ya yi tasiri wajen assasa wutar rikicin addini da kabila da rashin jituwa tsakanin yankunan kasar nan. Wadannan matsoli da muka tsuguna muka haifa, su ne a yau muke fama da su.”
“Abin da ya kamata a ce mu yi bayan zabukan 2015 shi ne mu dauki gabarar dinke barakar da yakin neman zaben 2015 ya haifar. Amma sai ba mu yi hakan ba. Sai ma muka buge da yin fami ga raunikan da ma haifar da wasu da dama,” inji Rabaran Mathew Hassana Kukah.