Home Labarai Cire tallafin mai: Gwamnatin Kwara ta rage ranakun aiki zuwa kwanaki 3

Cire tallafin mai: Gwamnatin Kwara ta rage ranakun aiki zuwa kwanaki 3

0
Cire tallafin mai: Gwamnatin Kwara ta rage ranakun aiki zuwa kwanaki 3

Gwamnatin jihar Kwara a Najeriya ta amince da ɗaukar matakin wucin-gadi na rage adadin kwankin aikin gwamnati a jihar domin taimaka wa ma’aikata wajen rage raɗaɗin da janye tallafin man fetur zai haifar.

A cikin wani saƙon da sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar Murtala Atoyebi, ya sanya wa hannu aka kuma wallafa a shafin gwamnatin jihar na Facebook, ta ambato shugabar ma’aikata ta jihar, Mrs Susan Modupe Oluwole na bayyana matakin,

Mrs Oluwole ta ce gwamnan jihar Abdulrahman Abdulrazaq ne ya bayar da umarnin rage kwanakin aikin gwamnatin na wucin-gadi daga kwana biyar zuwa kwanaki uku a kowane mako.

Mrs Oluwole ta umarci jagororin ma’aikatu da hukumomin gwamnati a faɗin jihar da su gaggauta tsara wa ma’aikatan hukumominsu kwanakin da ya kamata su je aiki.

Shugabar ma’aikatan jihar ta kuma gargaɗi ma’aikatan da kada su tozarta wannan karamcin da gwamnan jihar ya yi musu, tana mai cewa za a tsananta lura da kai ziyara ma’aikatu domin tabbatar da cewa ana bin dokar yadda ya kamata.

Sabon shugaban ƙasar ne dai ya sanar da matakin janye tallafin man fetur faɗin a jawabin da ya gabatar bayan shan rantsuwar kama aiki.

Matakin da ya haifar da tashin farashin man a fadin kasar, abin kuma ya sa direbobi suka ninka kudin mota a ƙasar, lamarin da masana ke ganin zai haifar da tashin farashin kayayyaki a ƙasar.

Tuni dai ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar NLC tare da wasu ƙungiyoyin suka yi barazanar shiga yajin aiki matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta janye matakin cire tallafin man fetur ɗin ba.