
Gwamnatin Ogun ta amince da biyan ƙarin Naira dubu 10 a kan albashin kowane ma’aikacin gwamnati da ɗan fansho, Tokunbo Talabi, Sakataren Gwamnatin Jihar, SSG, ya sanar.
Talabi, a wata sanarwa da ya fitar da yammacin jiya Litinin a Abeokuta, ya ce an tsara matakin na tsawon watanni uku.
Ya kara da cewa an yi hakan ne domin taimakawa ma’aikata su rage raɗaɗin matsin tattalin arzikin da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur.
“Wannan matakin ya yi daidai da abubuwan da ke faruwa a kasar nan da kuma kudirin gwamnatin jihar na inganta illar cire tallafin man fetur ga rayuwar al’ummar jihar,” in ji SSG.
Ya kara da cewa za a fara biyan kudin tallafin daga watan Yuli, yana mai bayyana cewa gwamnatin jihar ma za ta fara bayar da tallafin abinci ga wadanda ake ganin ba su da karfi.