
Majalisar Ƙoli, NEC, ta Ƙungiyar Ƴan Ƙwadago, NLC ta zartas da shawarar cewa za ta tsunduma cikin gagarumar zanga-zanga a faɗin ƙasa a ranar 1 ga watan Febrairu domin nuna rashin goyon bayan shirye-shiryen da gwamnatin Nijeriya ke yi na cire tallafin man fetur gaba ɗaya.
Ƙungiyar ta yanke shawarar ne a wani jawabin bayan taro da ta fitar a juya Juma’a, wanda Shugaban ta na ƙasa, Ayuba Wabba da kuma Babban Sakataren ta, Emmanuel Ugboaja su ka rattabawa hannu bayan taron majalisar zartarwar.
NLC ta ce kafin zanga-zangar ta ƙasa, reshinan ta na jihohi za su fara yin gangami a baki ɗaya jihohi 36 da ƙasar nan a ranar 27 ga watan Janairu domin nuna rashin goyon baya ga cire tallafin man fetur.
Jawabin bayan taron ya nuna cewa cire tallafin man fetur zai jefa ma’aikata da ƴan ƙasa cikin halin ni-ƴa-su sannan ya ƙara ta’azzara hauhawar farashin kayaiyaki da ya ke damun ƙasar.
“Sabo da haka ne majalisar ƙoli ta yanke shawarar ƙin amincewa da ƙarin farashin man fetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi domin ya nuna rashin tausayi ga wahalar da ƴan ƙasa da ma’aikata su ka tsinci kansu a ciki a ƙasar nan.
“Rashin yarda da amincewa na ƙarin farashin man fetur ne ya sanya za mu shirya zanga a gaba ɗaya jihohi 36 na ƙasar nan a ranar 27 ga Janairu.
“Da ga bisani kuma su mu rarraba wasiƙar gaiyata ga dukka gwamnoni jihohi 36, inda da ga bisani kuma sai mu fito zanga-zangar ta ƙasa a ranar 1 ga watan Febrairu a Abuja,” in ji jawabin bayan taron.
Ƙungiyar ta kuma shawarci gwamnatin taraiya da ta gyara matatan man fetur ɗin ƙasar nan domin amfanin ƴan ƙasa, maimakon cire tallafin man fetur da zai ƙara gallazawa talakawa.