
Wata ƙungiya mai zaman kanta da ke rashin sake da yancin ƴan kasa mai suna CISLAC ta roƙi zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya soke yarjejeniyar jinginar da filayen jirgin saman Kano da Abuja daga ranar da ya karbi mulki.
A wata sanarwar da ya sanya wa hannu, Babban Daraktan ƙungiyar, Auwal Musa Rafsanjani ya ce yarjejeniyar jinginar da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu, ba a yi ta da son ran yan ƙasa ba.
Ya ce bai kamata bayan an ranto kudade domin bunkasa filayen jirgin saman kuma kawai sai a ɓuge da jniginar da su ga turawa.
Ya nuna takaicin cewa filayen jirgin saman da su ke daya daga cikin manya-manyan kadarorin kasa, amma za su kwashe shekaru 50 a hannun Turawa.
Rafsanjani ya sake nuna takaici cewa filin jirgin sama na Kano na tarawa gwamnatin tarayya dala miliyan 700 a shekara,inda na Abuja ya ke tara dala miliyan 97.4.
“Wajen dala miliyan 800 kenan amma abin haushi Nijeriya za ta karbi kasa dala miliyan 10 a matsayin kudin jingina. Za ta karbi dala miliyan 7 a kan na Abuja sannan dala miliyan 1.5 a kan na Kano.
“Wannan cuwa-cuwa ce kuma ya kamata a yi duba a kai,” in ji shi.