Home Wasanni Ciwon zuciya ya tursasa Aguero yin murabus da ga ƙwallon ƙafa

Ciwon zuciya ya tursasa Aguero yin murabus da ga ƙwallon ƙafa

0
Ciwon zuciya ya tursasa Aguero yin murabus da ga ƙwallon ƙafa

 

Ɗan wasan gaban Argentina, Sergio Aguero, ya yi murabus da ga ƙwallon ƙafa.

Aguero ya yanke shawarar yin murabus ne sakamakon ciwon zuciya.

Aguero, wanda ya sauya sheƙa zuwa Barcelona da ga Manchester City a kakar wasa ta bana, ya tabbatar da cewa ya yanke hukunc ne mai wahala na yin murabus, maimakon yin ya yiwa lafiyarsa ganganci.

Ya ce ya na alfahari da iya dadewar da ya yi ya na harkar kwallo, bayan da ya tsinci kansa a cikin wani m byayuwacin hali, na rashin lafiya da ta sanya ya jingine takalmansa ala dole.

Ya kuma ce,”Na yanke wannan shawarar ne, saboda lafiya ta kawai”. Inji Aguero.

Aguero, ya dai jingine takalman sa daga harkokin kwallon kafa, bayan da ya buga wasanni 427 ya kuma ci kwallaye 786.

Cikin hawaye Aguero ya yi ban kwana da harkar kwallon kafa, inda ya godewa Ƙungiyoyin Ƙwallon Ƙafa kamar su Atletico Madrid and Manchester City, inda a nan ne ya fara rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.