Home Siyasa Ciyaman ɗin APC na Jihar Adamawa ya yi murabus

Ciyaman ɗin APC na Jihar Adamawa ya yi murabus

0
Ciyaman ɗin APC na Jihar Adamawa ya yi murabus

 

 

 

Shugaban jam’iyar APC na Jihar Adamawa, Ibrahim Bilal ya ajiye shugabancin jam’iyyar.

Tuni dai jam’iyar ta naɗa Samaila Tadawus a matsayin shugaban riko a jihar.

Bilal, a wata wasiƙa mai dauke da kwanan watan 13 ga watan Satumba, zuwa ga Sanaga Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ta ofishin mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa-maso-Gabas ya yi murabus daga muƙaminsa.

Wasikar ta ce: “Na rubuta wannan wasiƙa ne domin sanar da ku cewa na yi murabus daga mukamina na shugaban jam’iyyarmu ta APC na Adamawa nan take.

“Yayin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya bukaci in ci gaba da zama a ofishin har zuwa 2026, zan yi godiya idan har zan muƙami na a matsayin shugaban jam’iyar a jihar nan take.

“Ina neman afuwa idan har wannan matakin da na ɗauka ya ɓata wa wani ko haifar da rashin jin dadi,” in ji shi.

Ya kuma nuna godiya ga shugabancin jam’iyyar bisa damar da aka ba shi na yin aiki a jihar, musamman ma ya godewa shugabannin jam’iyyar na kasa da suka karbe shi.

Bilal ya kuma bada tabbacin yin biyayya ga manufofin jam’iyyar ba tare da ɓata lokaci ba, ya kara da cewa zai yi duk mai yiwuwa bisa doka don ci gaba da tafiyar jam’iyar.