Home Wasanni Conte ya bayyana abinda ya fadawa Messi bayan wasan jiya

Conte ya bayyana abinda ya fadawa Messi bayan wasan jiya

0
Conte ya bayyana abinda ya fadawa Messi bayan wasan jiya

Daga Hassan AbdulMalik

Kocin Chelsea, Antonio Conte ya bayyanawa manema labarai abinda ya fadawa Lionel Messi bayan karawarsu ta daren jiya a gasar zakarun turai zageye na 16 da aka buga a Camp Nou.

Conte ya ce a gaisawar da suka yi da Messi bayan wasan na jiya, ya yabawa dan wasan ne bisa yadda ya taka leda a karawar da ta yi sanadiyyar cire Chelsea daga gasar.

Messi ya zura kwallaye biyu kuma ya taimakawa Ousmane Dambele ya zura daya, wanda ya kawo sakamakon gasar zuwa 4 da 1 gida da waje.

Conte ya nemi Messi bayan wasan a lokuta har biyu daban-daban, inda ya yi musabiha da shi kuma aka ga yana fada masa wata magana, kafin daga bisani kuma ya rungume shi.

A lokacin da aka tambaye Conte abinda ya fadawa Messi a ‘yar gajiriyar tattaunawar da ake yi da kwace-kwacai da ‘yan wasan da suka yi rawar gani na bayan wasa, sai ya kada baki ya ce, “Damar yabawa Messi, dama ce ta yabawa kwararren dan wasa aji na farko.”

“Magana a ke yi akan dan wasan da a kowace shekara ya ke zura kwallaye akalla 60 a tsawon shekaru da dama yana ci gaba da haka,”

“Na yi matukar farin cikin samun damar ganawa da shi a karshen wasanmu don na jaddada masa matsayin ko shi waye shi.”

Magana muke game da dan wasa na musamman, wanda ba shi da tamka a duniya.”