Home Wasanni Cristiano Ronaldo ya bayyana dalilinsa na son barin Real Madrid a bana

Cristiano Ronaldo ya bayyana dalilinsa na son barin Real Madrid a bana

0
Cristiano Ronaldo ya bayyana dalilinsa na son barin Real Madrid a bana

Daga Hassan Y.A. Malik

Dan wasan gaba na Real Madrid, Cristiano Ranaldo, na son barin kungiyarsa ta Real Madrid saboda wani dalili nasa na kashin kai da ya dade yana damunsa.

Dalilin na Ronaldo dai bai wuce yadda takwarorinsa na Barcelona Lionel Messi da PSG Neymar Jnr suka fi shi daukar albashi ba.

Kafar Sky Sports ta rawaito cewa, ba wai Ronaldo na cikin wata damuwa bane ko yana da matsala da hukumomi ko abokan wasansa a Real Madrid, a’a! Matsalarsa daya ita ce, shi yana daukar albashin fam dubu 350 a mako, amma Neyamr na daukar fam dubu 600, Messi kuma na daukar fam dubu 750.

Wannan dai na zuwa na bayan da dan wasa  Ronaldo ya yi wani jirwaye mai kamar wanka inda ya bayyana rayuwarsa a Real Madrid a matsayin wani abu da ya gabata.

Ronaldo ya yi wannan batu ne a bayaninsa na bayan wasan karshe na cin kofin zakarun turai da suka buga da kungiyar Liverpool, inda Madrid ta lallasa Liverpool da ci 3 da 1.