Home Kanun Labarai Cutar zazzabin Lassa ta ɓulla a jihohi 18

Cutar zazzabin Lassa ta ɓulla a jihohi 18

0
Cutar zazzabin Lassa ta ɓulla a jihohi 18

Daga Hassan Y.A. Malik

Zazzabin Lassa na ci gaba da yaduwa a sassan kasar nan inda zuwa yanzu rohotanni ke nuna cewa akwai akalla mutane 1,081 da ke fama da cutar a fadin Nijeriya baya ga mutum 90 da suka rasa rayukansu a jihohi 18 da cutar ta bulla.

Wannan bayani na kunshe ne a wata sanarwa da Cibiyar Lura da Cututtuka ta Nijeriya, NCDC, ta fitar a jiya Talata, inda snarwar ke cewa, akalla mutum 54 suka kamu da cutar a cikin mako guda, inda cutar ta sake bulla a jihohi 8 da a da babu, haka kuma aka sake samun rahoton mutuwar mutum 10 a jihohi 5.

Sanarwa ta ci gaba da cewa dukkan mutane 1,081 da aka samu da cutar a baya-bayan nan sun dauki zazzabin daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa ranar 25 ga watan Fabrairun 2018, kuma mace-macen sun faru ne a jihohin: Edo, Ondo, Bauchi, Nassarawa, Ebonyi, Anambara, Binuwai, Kogi, Imo, Filato, Legas, Taraba, Delta, Osun, Ribas, Abuja, Gombe da jihar Ekiti

Kaso 43 daga cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar zazzabin Lassa daga jihar Edo suke, sai jiha mai bi ma ta ita ce jihar Ondo mai kaso 26 cikin 100 na adadin mutanen da ke dauke da cutar.

Ma’aikatan lafiya da wadanda ke kula da marasa lafiyar guda 14 sun kamu da cutar a jiho 6. Ma’aikatan lafiya 7 daga Ebonyi, 1 daga Nassarawa, 1 daga Kogi, 1 daga Binuwai, 1 daga Ondo, sai 3 daga Edo. Haka kuma mutane 4 ne daga ma’aikatan lafiyar suka rasu, 3 daga Ebonyi, 1 daga Kogi.