
A jiya Lahadi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Legas, Abdulazeez Adediran (Jandor), ya tsallake rijiya da baya, yayin da wasu ƴan daba suka kai wa tawagar yakin neman zabensa hari.
Wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Hakeem Amode ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na yamma, yayin da ayarin yakin neman zaɓen ke dawo wa daga ziyarar da ya kai ga ƴan jam’iyyar PDP a unguwar Ikoga Junction da ke Ƙaramar Hukumar Badagry.
Sanarwar ta ce an kai wa tawagar jam’iyyar PDP hari, ciki har da ƴan jarida, inda ta ce ɗaya daga cikin ƴan jaridar ma na cikin mawuyacin hali a wani asibiti da ba a bayyana ba, yayin da wasu kuma ke samun kulawa.
“Hakan ya faru ne a daidai lokacin da mai magana da yawun jam’iyyar ya tuna da cewa kwanan nan ya nuna damuwa kan barazanar yin amfani da ƴan daba wajen kai hari kan shirye-shiryen yakin neman zaben Jandor, dan takarar gwamna na PDP, amma ya ce irin wannan lamarin ba zai “sare mana gwiwa a kudurin dan takararmu, Kamfen na zabe mai zuwa da kuma lashe zaben na zuwa ranar 11 ga Maris, 2023 ba,” in ji sanarwar.
“Za ku tuna cewa jam’iyyarmu ta nuna damuwa kan barazanar amfani da ‘yan daba wajen kai hari kan shirye-shiryen yakin neman zaben dan takarar gwamnan mu Dr. Abdul-Azeez Olajide Adediran- Jandor kwanan nan.
“Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa hakan ba zai hana dan takararmu yin yakin neman zabe ba
“Don haka jam’iyyar ta yi kira ga kwamishinan ƴan sanda na jihar Legas da kuma kwamandan ƴan sanda na yankin Badagry da su yi duk mai yiwu wa don kakkabo wadanda suka kai harin, tare da tabbatar da cewa an dauki matakin ladabtarwa a kansu don dakile. irin abubuwan da suka faru a nan gaba.
Sanarwar ta ce yin hakan zai sanya wa ƴaƴan PDP kwarin gwiwa cewa za a kare su a wannan lokacin yakin neman zabe,” in ji shi.