Home Siyasa Ƴan daban siyasa sun jefi Kwankwaso a Kogi

Ƴan daban siyasa sun jefi Kwankwaso a Kogi

0
Ƴan daban siyasa sun jefi Kwankwaso a Kogi

 

 

Wasu ƴan jagaliyar siyasa, a jiya Laraba sun jefi dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso da ruwan leda yayin da ya kai ziyara jihar Kogi.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Kwankwaso ya je Lokoja, babban birnin jihar domin kaddamar da sakatariyar jam’iyyar da ofisoshin yakin neman zabensa.

A lokacin da ya isa wani otel da zai yi jawabi ga magoya bayansa, wasu da ake zargin ’yan daba ne suka mamaye wurin, suka fara jifan dan takarar da ruwan leda.

Tun da fari, Kwankwaso ya ziyarci Ogbonicha, mahaifar marigayi Abubakar Audu, inda aka yi irin wannan lamarin.

Ƴan siyasar garin na zargin shi da kokarin fakewa a karkashin inuwar tsohon gwamnan don jan hankalin magoya bayan jam’iyyar APC.

Wani mai taimaka wa dan takarar shugaban ƙasar, kan harkokin yada labarai, wanda ya bayyana kansa a matsayin Musa Yunusa, ya bayyana abin da a ka yi wa Kwankwaso a matsayin al’adar siyasa, inda ya bayyana Kogi a matsayin gida ga Kwankwaso.