Home Labarai Daga kasar Faransa, Shugaba Buhari ya zarce Afirka ta Kudu don halartar kasuwar baje koli

Daga kasar Faransa, Shugaba Buhari ya zarce Afirka ta Kudu don halartar kasuwar baje koli

0
Daga kasar Faransa, Shugaba Buhari ya zarce Afirka ta Kudu don halartar kasuwar baje koli

 

A yau Asabar ne Shugaba Muhammadu Buhari ya zarce birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu don halartar bude kasuwar baje koli ta kasashen Africa, wato “2nd Intra-African Trade Fair 2021”.

A sanarwar da kakakin fadar shugaban kasa Femi Adesina ya fitar a yau, shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya mika wa Buhari goron gayyata.

Za’a bude kasuwar baje kolin ne daga ranar 15 zuwa 21 ga wannan wata na Nuwamba.

Tun ranar 1 ga watan Nuwamba Shugaba Buhari ya bar Najeriya don halartar taron gangami kan canjin yanayi wato “COP 26” a birnin Glasgow na kasar Scotland.