
Kwamitin gudanarwa na Masallacin Juma’a na Apo da ke Abuja ya dakatar da Babban Limamin masallacin, Sheikh Nuru Khalid, saboda sukar da ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harin bam na jirgin kasa na Kaduna.
Limamin, a cikin huɗubarsa ta jiya Juma’a, ya soki shugaban kasa kan gazawar sa ta zuwa Kaduna don jajanta wa waɗanda harin ta’addancin da aka kai ya rutsa da su.
Ya ce shugaban ya je Kaduna domin yakin neman zaɓe, amma ya ƙi zuwa jihar bayan harin bam don ya jajantawa al’umma.
“Shugaban kasa Buhari ya ce wai yana Allah wadai, in banda su ƴan ta’addan, kowa ma ai yayi Allah wadai da faruwar lamarin. Ya kamata shugaban kasa ya ziyarci jihar domin jajantawa wadanda abin ya shafa”. Inji Malamin
Sai dai kuma Shugaban kwamitin kula da masallacin, Sai’du Dansadau, ya ce an dakatar da malamin ne sabo da hudubar da yayi a ranar 1 ga Afrilu za ta iya tunzura al’umma.
Ya bayyana cewa Shehun Malamin ya yi wa’azi na hana al’umma yin abun da kundin tsarin mulkin ƙasa ya basu, ta hanyar shawartar masu zabe da su baiwa ƴan siyasa sharadi kafin zaben su.
Dansadau ya kuma kara da cewa wa’azin ya sabawa tsarin addinin Musulunci.