
Dokta Mohammed Danjuma, Ko’odinetan shirin farfado da Arewa-maso-Gabas da ta sha fama da rikice-rikice a Nijeriya, MCRP, ya ce kimanin dala miliyan biyu aka kashe wajen gudanar da ayyuka a yankin.
Danjuma ya bayyana haka ne a wani taron karawa juna sani na kaddamar da shirin gudanar da bincike da tallafawa hukumomi a karkashin bangare na uku na shirin karin kudade na MCRP a Abuja a jiya Laraba.
Ya bayyana cewa an kashe kudaden ne a matsayin gyara ga lamuran da suka shafi jihohin da abin ya shafa a yankin.
Ya ce inganta aiki zai kasance daya daga cikin muhimman dinadarai da ake bukata a jihohin da abin ya shafa.
Danjuma ya bayyana cewa ana kokarin inganta manyan makarantu da ma’aikatu da sassan jihohin da ke da alaka da tallafin bincike.
Ya ce kaddamarwar ta shafi tallafin bincike da shawarwari, inda ya ƙara da cewa sai da aka bi hanyar sahihiya ta tantance su.