Home Labarai Dalaget ɗin Jigawa ya rasu a wajen zaɓen fidda-gwani na APC a Abuja

Dalaget ɗin Jigawa ya rasu a wajen zaɓen fidda-gwani na APC a Abuja

0
Dalaget ɗin Jigawa ya rasu a wajen zaɓen fidda-gwani na APC a Abuja

 

Ɗaya daga cikin dalaget na jam’iyyar APC, reshen jihar Jigawa, Isah Baba Buji, ya yanke jiki ya faɗi ya kuma mutu a yayin da yake shirin zuwa dandalin Eagle Square, wurin da za a gudanar da zaɓen fidda-gwani na shugaban ƙasa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa Buji ya rasu ne a safiyar yau Talata a ofishin Jihar Jigawa a Abuja a sakamakon zargin ciwon zuciya.

Marigayin dai shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Jigawa ta tsakiya.

Jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar APC na jihar Jigawa, Bashir Kundu ya tabbatarwa da jaridar The Nation faruwar lamarin.

Ya ce: “Eh, ya rasu a safiyar yau. Ya yanke jiki ya faɗi a ofishin jihar Jigawa da ke Abuja, inda aka garzaya da shi asibiti, sai kuma ya rasu kafin ya isa asibiti.

“Lokacin da muka isa asibiti an tabbatar da cewa ya rasu. An ce ya mutu ne sakamakon ciwon zuciya.”