
Mai neman takarar gwamna jam’iyar PDP takarar gwamna a Jihar Kaduna a zaben 2023, Sanata Shehu Sani, ya ce daleget biyu ne rak su ka zaɓe shi a zaɓen fidda-gwani.
Shehu Sani ya kuma bayyana cewa ko sisinsa bai baiwa waɗannan daleget biyun da su ka zaɓe shi ba.
Sanata Sani ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau Alhamis.
A cewarsa, bai san su wadannan daleget biyun da su ka zaɓe shi ba, yana mai cewa deleget kusan 300 ne suka kira shi suna masu bayyana masa cewa suna cikin mutum biyun da suka zabe shi.
Ya taya Honorabul Isah Ashiru, mutumin da ya lashe zaben.