
Akalla dalibai 20 ne suka rasu tare da wasu daga cikin Malamansu na makarantar Sakandiren Gwamnati dake Misau. Daliban sun yi hadari ne akan hanyarsu ta zuwa Kano daga Misau.
Wani da yaga abin ya bayyana cewar motar dake dauke da daliban mai cin mutane 18, tayi daga daga. Har ya zuwa yanzu da muke hada wannan rahotohukumomin ilimi na Gwamnatin jihar Bauchi basu ce komai ba.