Home Kasuwanci Dalilin da ya sa mu ka ƙara farashin cirar kuɗi — Masu POS

Dalilin da ya sa mu ka ƙara farashin cirar kuɗi — Masu POS

0
Dalilin da ya sa mu ka ƙara farashin cirar kuɗi — Masu POS

Wasu masu sana’ar PoS, sun yi zargin cewa jami’an banki su na sayar musu da tsoffi da sabbin takardun kudi, daidai da adadin da kwastoma zai cire a banki.

Wasu daga cikin masu POS da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Abuja a jiya Juma’a, sun ce suna biyan makudan kudade domin cire kudade, shi ya sa suke kara wa kwastomomi farashin cirar kudi.

Sun kuma yi kira ga babban bankin Najeriya CBN da ya hukunta bankunan da ke da hannu a wannan ta’ada.

Wata mai POS a kan hanyar Nyanya-NNPC, wadda ta nemi a sakaya sunanta ta ce ta na biyan karin kudaden ne domin kar sana’arta ta tsaya.

“Na biya kudi mai yawa don samun wannan kuɗin da nake ba abokan ciniki. Idan ka duba a nan, wasu masu aiki ba su buɗe ba.

“ita ma’aikaciyar bankin da na ke karbar kudi a hannunta ma ta kara kudin a yau saboda ta ce tsabar kudi ta yi karanci kuma ta ajiye min saboda na kira ta tun da farko na ce ta ajiye min.

“Ina biya bisa ga adadin da na karba. Wani lokaci nakan biya N5,000 akan N50,000 zuwa N70,000 da nake karba a wajen ta.

“Ina karbar Naira ɗari 5 ga duk Naira dubu 5 da aka cire, sannan N1000 kan duk N10000 da aka cire min domin na mayar da abin da na kashe wajen samo kudin,” inji ta.