
Ƙungiyar ATIKU/OKOWA VANGUARD 2023, ta ce ɗan Takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar PDP a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya fi dukkanin ƴan takarar kujerar dacewa.
Shugabannin jihohi na ƙungiyar, su ne su ka bayyana hakan, a wata ziyara da su ka kai wa Atiku, kamar yadda Abdulrasheed Shehu, Mataimaki na Musamman ga Atiku ya faɗa a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a jiya Talata.
Sun ce Atiku na da dukkan ƙwarewar da ake buƙata don ceto Najeriya tare da sauya al’amuran jama’a domin su koma daidai.
Wakilan wannan ƙungiya sun ce suna da wannan tabbaci ne saboda irin tarihin gogayya da kwarewar da Atiku yake da ita a harkar kasuwanci da shugabancin jama’a.
Babbban daraktan kungiyar, Hon. Sam Amonu, lokacin da ya jagorancii ayarin kungiyar zuwa ziyara ga Atiku Abubakar, yace tsohon mataimakin shugaban kasar shi ne zabi Mafi dacewa domin kubutar da Najeriya Daga halin da take ciki.
Ita ma a nata bangaaren, shugabar kungiyar ta kasa Dr (Mrs) Obi Nwaogu tace manufar ziyarar ita ce isar da godiyarsu ga Atiku Abubakar a kokarin da yake na karfafa tsarin dimukuradiyya a Najeriya.
Tace suna da kyakkyawan fata akan Atiku da Okowa domin gwamnatin su zata ceto Najeriya.