Home Labarai Dalilin da ya sa Ethiopia ta dakatar da biza ga ƴan Nijeriya lokacin sauka ƙasar — Gwamnati

Dalilin da ya sa Ethiopia ta dakatar da biza ga ƴan Nijeriya lokacin sauka ƙasar — Gwamnati

0
Dalilin da ya sa Ethiopia ta dakatar da biza ga ƴan Nijeriya lokacin sauka ƙasar — Gwamnati

 

 

 

Gwamnatin Tarayya ta ce Ethiopia ta dakatar da bada biza a lokacin sauka ƙasar ga baki ƴan kasashen waje a duk wuraren shiga ya faru ne saboda rashin tsaro, musamman dangane da yanayin siyasar kasar.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen, Francisca Omayuli ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a jiya Alhamis a Abuja.

Sai dai gwamnati ta bukaci ƴan Nijeriya da ke da niyyar zuwa Habasha don samun bizar da ta dace a ofishin jakadancin kasar ko ta hanyar yanar gizo (e-visa) ta Hukumar Shige da Fice ta kasar, ICS, ta adireshin yanar gizo ta www.evisa.gov.et .

“Dakatar ta shafi dukkan ‘yan kasashen da ke ɗauke da fasfot, wadanda ke neman shiga kasar Habasha ba musamman kan ƴan Najeriya ba.

Omayuli ta ce “Hukumomin Habasha sun yi bayanin cewa matakin na da nufin inganta iyakoki na zirga-zirgar mutane zuwa Habasha saboda rikicin da ke faruwa a Arewacin kasar,” in ji Ms Omayuli.

Ta kuma bayyana cewa matakin na wucin gadi ne, har sai an samu ci gaba a harkokin tsaro a kasar, inda ta ce hakan ba wai na nufin maye gurbin manufar bude biza ta kasar Habasha ba.