Home Ƙasashen waje Dalilin da ya sa na hana ministoci na ƙara aure — Shugaban ƙasar Nijar

Dalilin da ya sa na hana ministoci na ƙara aure — Shugaban ƙasar Nijar

0
Dalilin da ya sa na hana ministoci na ƙara aure — Shugaban ƙasar Nijar

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, ya ce ya hana dukkanin ministocinsa ƙara aure ne a matsayin wani mataki na magance talauci da rage haihuwa a kasar.

A cewar bankin duniya, kasar na ɗaya daga cikin kasashen da su ka fi fama da tsananin talauci a yammacin Afirka da ke da matakin tattalin arzikinta, GDP dalar Amurka 567.7 ne kacal da kuma yawan al’umma miliyan 25.

A wata hira da ya yi da rediyon VOA, Bazoum, wanda ke birnin Washington don halartar taron Amurka da Afirka, ya dora alhakin yawaitar jahilci da ake fama da shi a kasar ne sanadiyyar ƙaruwar al’umma.

Ya ce hatta kasashen Larabawa da al’ummarsa suke kallon su a matsayin alƙibla wajen gudanar da addinin Musulunci, ba sa haihuwa da yawa.

“Labawa abin koyi ne a cikin wannan addini (Musulunci). Amma da kyar ka sami yara sama da uku a gida, kowane iyali yana da ‘ya’ya biyu ko mafi girman ’ya’ya uku, kuma haka lamarin yake a dukkan kasashen Larabawa da Musulmi.

“Amma mu a namu ɓangaren, za ku sami yara 10, 20 har ma 30 a gida daya, wannan shine matakin farko na talauci,” in ji Bazoum.

“Babban dalilin hakan shi ne, mutanenmu ba su da ilimi. Da yawa daga cikinmu ba su je makaranta ba, kuma idan ka nemi ilimi ne za ka fahimci cewa haihuwa da yawa zai kai ka ga talauci.

“Dauki manyan mutane misali: ministoci, shugabannin tsaro, da manyan jami’an gwamnati. Ba za ka tarar sun haifi yara 30 a gidajensu ba, kuma wadannan su ne masu hannu da shuni a cikin al’ummarmu.

Da aka tambaye shi ko hakan ne ya sa ya yanke shawarar haramta wa ministocinsa ƙarin aure, Mista Bazoum ya amsa da cewa eh haka ne.

Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wani ɗan majalisar ministocin da ya yi niyyar auren karin mata, dole ne ya yi watsi da nadin nasa.

“Eh, na ba da wannan umarni, ba za ka iya zama minista a gwamnatina ka auri mata biyu ba, kuma babu daya daga cikinsu da ya karya wannan umarni.

“Duk da haka, wadanda suke da mata biyu kafin su hau mulki an basu damara su ci gaba da zama da su,” in ji shi.