
Mawakan arewa sun kafa wata sabuwar kungiya da suka yi wa sunan tatin-tatin (13×13) domin taimaka wa sassan ci gaban al’umma.
A cikin wata sanarwa daga sakataren kungiyar, Hashim Abdallah, an bayyana cewa, “Kungiya ce da mutum 13 suka samar da ita kuma alkhairi ce ga al’umma kamar yadda taken tafiyar yake.
Sanarwar, wacce a ka fitar da ita a jiya Juma’a, ta ce an yi imani tafiyar za ta inganta rayuwar ƴan Nijeriya domin samar da rayuwa mai inganci ko inganta rayuwar ta fuskoki daban-daban gaba da siyasa ko wakar siyasa ko kamfe.
“13×13 Ba ta da wani makiyi sai makiyin al’umma. A dalilin hadafi na ‘yanta kasa, lallai 13×13 ta kafu ne mahadi-ka-ture wato har illa mashaAllahu.
“Wannan yunkuri ne da manufar dago da masu fasaha da masu baiwa, daga mawaka, marubuta jaruman fim, ‘yan wasan kwaikwayo ko dago da darajar wadannan masu fasaha a kowane fage na basirar da Allah Ya ba su a siyasa ko waken al’uma ko wa’azi ko don harshe wato adabi a dunkule,” in ji sanarwar.
“Wannan kungiya tana da shugabanci mataki-mataki, kuma shugaba na kasa shi ne, Dauda Kahutu Rarara da Kwamitin gudanarwar jihohi na kasa karkashin babban mawaki ElMu’az Birniwa. Babban marubucin fina-finai Ibrahim Birniwa ya kasance shi ne mataimakin shugaban kwamitin siyasa na kasa da sauransu,” in ji sanarwar.