Home Siyasa Dalilin da ya sa na koma NNPP — Shekarau

Dalilin da ya sa na koma NNPP — Shekarau

0
Dalilin da ya sa na koma NNPP — Shekarau

 

Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.

Da yake taron manema labarai a Kano a jiya Laraba, Shekarau ya ce ya fice daga APC ne saboda shugabancin jam’iyyar a jihar ya gaza cika alkawuran da ya dauka na tafiya tare da shi da magoya bayansa a harkokin jam’iyar.

“Duk da irin gudunmawar da muka bayar, magoya bayan mu sun yi mamakin yadda a ke samun rashin yabawa da kuma ba a yi da mu a al’amuran jam’iyar.

“A matsayinmu na ‘yan jam’iyya masu kishin kasa kuma muna sane da ayyukan da muke da su a matsayinmu na mazauna jihar Kano, don baiwa gwamnati shawarwari da goyon bayan da ake bukata don samun nasara, mun jajirce kuma muka ci gaba da lalubo hanyoyin da za mu tuntuɓi gwamnati.

“Amma abin takaici, duk wannan ƙoƙarin namu bai samu karɓuwa ba, ƙarshe ma sai ka ga an sace mana gwiwa.

“Ganin hakan ne ya sanya mu ka yi duba na tsanani mu ka ga cewa wani yunƙuri ne da APC da gwamnati ke yi na ajiye mu a gefe da mu da magoya bayan mu,” in ji shi

Shekarau ya ƙara da cewa ba a gudanar da zaben shugabannin jam’iyya na jiha bisa ka’idojin da aka gindaya ba.

Ya kuma ce zai sake neman tsayawa takarar Sanata a jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023.