Home Siyasa Dalilin da ya sa ba zan yi takara ba — Adesina

Dalilin da ya sa ba zan yi takara ba — Adesina

0
Dalilin da ya sa ba zan yi takara ba — Adesina

 

Shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka, AfDB, Dakta Akinwumi Adesina, ya fitar da kansa daga takarar shugabancin Nijeriya a 2023.

A tuna cewa wata kungiya ce ta saya wa Adesina ɗin fom ɗin tsayawa takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC.

Sai dai a wata sanarwa a yau Talata, Adesina ya ce tarin Aiyuka da hada-hadar ofishinsaa bankin AfDB ba za su iya ba shi damar neman shugabancin ƙasa ba.

Ya ce: “na ji daɗi da karrama ni da a kai kuma ina mai godiya ga dukkan kyakkyawar niyya, kyautatawa, da kuma kwarin gwiwa, nauyin da ke kai na a yanzu ba zai ba ni damar tsaya wa takara ba” in ji sanarwar.

“i na ci gaba da ba da himma da hidima ga domin sauke nauyin da Nijeriya, Afirka, da duk masu hannun jarin da ba na Afirka ba na Bankin Raya Afirka suka ɗora mini don ci gaban Afirka.

“Na ci gaba da mayar da hankali sosai kan manufar tallafawa ci gaba da bunkasa tattalin arziki na Afirka.”