Home Labarai Dalilin da ya sa ba a yi zanga-zanga a Zamfara ba — PDP

Dalilin da ya sa ba a yi zanga-zanga a Zamfara ba — PDP

0
Dalilin da ya sa ba a yi zanga-zanga a Zamfara ba — PDP

Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Zamfara ta ce zanga-zangar matsin rayuwa ba ta karaso jihar ba sakamakon kyakkyawan mulki da Gwamna Dauda Lawal Dare ke yi a jihar.

Mukaddashin shugaban jam’iyar a Zamfara, Mukhtar Lugga ne ya baiyana haka a wata hira da manema labarai a Gusau a jiya Jama’a.

Ya ce al’ummar Zamfara sun gamsu da yadda gwamnan ke tafiyar da gwamnatin sa saboda an samu nasarori da dama.

A cewar sa, gwamnatin gwamna dare ta samar, kuma ta na kan hanyar samar da shirye-shirye da manufofi na inganta rayuwar al’umma.

“Ta ƙaddamar da dokar ta ɓaci a kan ilimi da lafiya. Ta biya kudaden yan ga shi gaba dayan sh.

“Gwamnatin sa ta gina da sake gina tituna. Ta gayara tare da fente makarantu da asibitoci. Ga kuma yadda ya fado da sana’ar noma a fadin jihar.

Ya ƙara da cewa duk da ana fama da matsin rayuwa a Nigeria, gwamnatin Dare ta taka rawar gani wajen rage wa al’umma wannan wahalhalu.