
Jagoran jam’iyar APC na Ƙasa, kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce goranta wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari cewa ba dan ya mara masa baya ba da ba zai kashe zaɓen 2015 ba.
Daily Trust ta rawaito cewa Tinubu ya bayyana haka ne a Abeokuta yayin gana wa da dalaget gabanin zaɓen fidda-gwani da ke tunkaro wa.
Ya ce “ba don ni ba da Buhari ba zai ci zaɓen 2015 ba. Ya faɗi a zaɓen farko, na biyu da na uku, har ma ya fito gidan talabijin ya ja cewa ba zai sake tsaya wa takara ba.
“Shi ne na je Katsina na sane shi, na ce masa sai ka sake tsaya wa kuma za ka ci. Amma da ya ci, sai ga shi ko minista ba a naɗa ni ba kuma ba a taɓa bani kwangila ba. Sabo da haka wannan karon na yarabawa ne kuma nine zan tsaya takara. Wannan karon nawa ne,” in ji Tinubu yayin da yanke faɗa wa dalaget ɗin da yaren yarabanci.
Tinubu ya kara da cewa lokacin da ya so ya zama mataimakin shugaban ƙasa, sai wasu ƴan adawa su ka kawo batun Musulmi-da-musulmi, shine a ka bashi dama ya kawo wanda zai yi takarar mataimaki.
A cewar Tinubu, mutane uku ya samu yai musu maganar takarar da su ka haɗa da, Yemi Kadoso, Wale Edun da kuma Yemi Osinbajo, inda ya ce a karshe dai Osonbajo ya samu nasara.
Tinubu ya ƙara da cewa tunda ya ke bai taɓa fadar wannan maganar ba sai yanzu.