Home Kanun Labarai Dan kunar bakin wake ya kashe masu Sallar Tahajjud a Maiduguri

Dan kunar bakin wake ya kashe masu Sallar Tahajjud a Maiduguri

0
Dan kunar bakin wake ya kashe masu Sallar Tahajjud a Maiduguri

Wani dan kunar bakin wake da ya layyace jikinsa da Bom ya kashe dan kungiyar ‘yan gora ta Maiduguri guda dayada aka fi sani da sunan ‘Civilian JTF’ sannan kuma ya jikkata wasu mutum da suka fito Sallar Tuhajjud a kan titin Baga dake cikin garin Maiduguri.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Wakil Maye, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari ga manema labarai a Maiduguri ranar Litinin, yace abin ya auku ne da misalin karfe 1 na dare.

Maye yace, ‘yan kungiyar ‘Civlan JTF’ ne suka gano dan kunar bakin waken daga nesa a lokacin da ya dumfaro inda jama’a suke.

“Dan kunar bakin waken ya kasa karasawa inda yayi nufi, wannan ta sanya yayi saurin tayar da bom din da yake jikinsa, ya kashe kansa sannan ya kashe dan kungiyar ‘yan gora, sannan kuma ya jikkata wasu karin mutum hudu”