
Dan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar karamar hukumar Bakura, Saidu Yarkufoji ya rasa mutane goma daga cikin iyalansa sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da su, a cewar jami’an kula da hanya na FRSC reshen jihar Zamfara.
Bayanai sun tabbatar da cewar dan majalisar yayi rashin ‘ya ‘yansa guda uku, sai kuma jikokinsa guda hudu da kuma kannensa mata guda biyu da kuma direbansa a sakamakon wannan hadari da ya rutsa da su akan hanyar Sakkwato zuwa Gusau.
An dai yi taho mu gama ne, tsakanin wata motar kamfanin koka kola da kuma kramar motar da iyalan dan majalisar suke ciki. Tuni dai aka yiwa iyalan dan majalisar Sutura aka kuma yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.